Forgotten Dairies
Ya Kamata A Dinga Tallafawa Gajiyayyu, Tare Da Wayar Wa Al’umma Kai, Wajan Kiyaye Kamuwa Daga Cutar Corona Virus -By Adamu Usman Garko

Ya kamata gwamnati ta kirkiri wata Kungiya da zata dinga wayar da kan mutanen cikin gari da na karkara, kan yadda zasu dinga kiyaye kansu da samun kariya wajan kamuda daga cutar Corona Virus.
Mafi yawan mutanan da suke rayuwa cikin gari da karkara, basu san yadda zasu dinga kiyaye kansu daga kamuwa da cutar ba.
Kamar yadda naga abun mamaki, inda jiya naga wani bawan Allah, a bakin hanya ya mika wa abokin shi Hannu da zummar su gaisa, abokin nashi yaki gaisawa dashi, sai kawai ya dauko Facemask dinshi ya Saka a fuska, sai ya sake mikawa abokin nashi hannu domin su gaisa.
Duk tunanin shi Saka facemask na hana kamuwa da cutar, ko da kunyi hannu da mutum, wani kuma bai damu da Saka facemask din ba, don kariya daga cutar ba. Kawai shi yana saka facemask ne din bin doka, ba don samun kariya daga cutar ba.
Muna kira ga gwamnati da masu madafun iko, da suyi amfani da kungiyoyi masu register domin tallafawa mutane, wajan shiga lungu da sako, don su wayarwa da mutane kai, game da wannan cutar da ta kunne kai jihar mu.
Yanzu lokaci ne da zamu ajiye dukkanin bambance-bambance na Addini ko na siyasa, domin hada karfi da karfe wajan wayar wa da Mutane kai, game da wannan Annobar da ta kunno yankinmu.
Lokaci ne da masu kudi zasu yi amfani da dukiyarsu wajan Tallafawa Marayu da mabukata, tare da gajiyayyu domin rage musu radadin da suke ciki.
Idan kowa yayi amfani da damar da Allah ya bashi, komin kan kantarta wajan Tallafawa Marayu da mabukata, hakan zaisa farin ciki a zukatan al’umma.
Muna Addu’ar Allah Ya Kawo Mana Karshen Wannan Annobar.